12 Satumba 2020 - 13:10
Kakakin Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen, Ya Ce; Ya Kamata A Haka Kabari A Binne Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa

Kakakin kungiyar ta “Kungiyar Ansarullah” ta kasar Yemen, Muhammad Abdussalam’ ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa; Idan har Palasdinu za ta to wajen kungiyar ta nemi ta fitar da wani matsayi, sannan ta kiya, to wannan kungiyar ta mutu ya kamata a haka kabari a rufe ta.

ABNA24 : Muhammad Abdussalam ya yi Allah wadai da babbar murya akan yadda kungiyar hadin kan kasashen larabawan ta ki yarda da bukatar Palasdinawa.

Kakakin na kungiyar Ansarulalh ya kuma ce; Al’ummun wannan yankin suna a raye, kuma kasashen da su ka yi tir da wannan matsayin na kungiyar hadin kan kasashen larabawa a cikin kungiyar su ne abin dogaru da jingina wajen goyon bayan hakkin palasdinawa.

A tsakiyar mako mai karewa ne dai kungiyar ‘yanto Palasdinu ta PLO ta bakin sakatarenta, Sa’ib Uraiqat ta yi barazanar ficewa daga cikin kungiyar Larabawan idan har ta amince da daftarin kudurin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gagabatar mata akan hulda da HKI.

342/